Monday, 27 August 2018

Firai minista Theresa May za ta ziyarci Afirka a karon farko

A karon farko firai ministar Birtaniya Theresa May za ta ziyarci nahiyar Afirka tun da ta fara shugabantar kasar a 2016.


Misis May za ta fara ziyartar Afirka ta Kudu ne ranar Talata kafin ta isa zuwa Najeriya da Kenya a cikin shirinta na bunkasa ciniki da nahiyar bayan Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai.

Ta ce wannan tafiyar za ta kasance wata babbar dama a lokaci mai cike da tarihi ga Birtaniya.

Ta kuma ce tana son bunkasa da karfafa danagantakar Birtaniyar da wasu sassa na duniya gabanin ficewar kasar daga Tarayyar Turai.

'Yan kasuwa 29 za su raka Misis May zuwa wadannan kasashen uku.

Ana kuma sa ran za ta tattauna akan batun tsaro bayan ta isa Najeriya - musamman rikicin Boko Haram da rawar da sojojin Birtaniya da aka girke a Kenya ke takawa wajen yaki da mayakan al Shabab a Somaliya.

A ranar Talata za ta isa birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, inda za ta gana da matasa, da 'yan kasuwa sannan akwai wani taron koli tsakaninta da shugaba Cyril Ramaphosa.

Za kuma ta ziyarci tsibirin Robben, inda aka tsare Nelson Mandela.

A ranar Laraba za ta isa Abuja domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari, kafin ta wuce zuwa birnin Legas.

A ranar Alhamis za ta isa birnin Nairobi na kasar Kenya domin ganawa da shugaba Uhuru Kenyatta, kana ta ziyarci dakarun Birtaniya da wata makarantar koyar da kasuwanci.

Wannan ziyarar zuwa Kenya zai kasance karon farko da firai wani shugaban kasar ya kai irin wannan ziyara tun ziyarar Margaret Thatcher a shekarar 1988.

Wannan ne kuma karon farko da ta kai ziyara zuwa yankin yamma da hamadar Sahara tun da tsohon firai minista David Cameron ya ziyarci Afrika ta Kudu a 2013.

Kakakin ofishin firai minista da ke Downing Street ya ce wannan ziyarar na da zummar karfafa tsaro da inganta zaman lumana a Afirka ne domin kasashen nahiyar na fuskantar kalubalen tsaro da na siyasa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment