Sunday, 12 August 2018

Gerard Pique ya daina bugawa kasarshi ta Sifaniya wasa

Tauraron dan kwallon kasar Sifaniya Gerard Pique ya ajiye bugawa kasarshi kwallo inda yace ya gaji da sukarshi da magoya bayan kwallon kafar kasar da kuma 'yan jarida ke yi, yana so a barshi ya huta.


Ya bayyana cewa ya gayawa me horas da 'yan wasa na kasar, Luis Enrique cewa ya daina buga musu kwallo, yaji dadin kasancewa daya daga cikin taurarin kwallon kasar da suka ciwo kofin Duniya da dana zakarun turai, dan shekaru 31 ya bayyana cewa yanzu yana so ya mayar da hankali akan kungiyarshi ta Barca ne a sauran lokacin da ya rage mishi, kamar yanda ya shaidawa manema labarai

No comments:

Post a Comment