Sunday, 5 August 2018

Gwamna Dankwambo Ya Aiyana Niyyar Neman Takarar Shugaban Kasa A PDP

Karshe dai gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya aiyana niyyar neman tikitin takarar shugabancin Najeriya a inuwar babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP.


Dankwambo dai ya kawo karshen watanni na bayanan cewa zai nemi takarar duk da cewa bai ambaci hakan kai tsaye da bakin sa ba.

Gwamnan dai da zai kare wa'adin sa na biyu na gwamna a Gombe a 2019, ya aiyana niyyar ce a taron wakilan zaben dan takara na PDP a shiyyar arewa maso gabas. 

Ibrahim Dankwambo dai na daga cikin gwamnoni kalilan koma a ce shi kadai ne da masu sharhi su ka ce guguwar Buhari ta 2015 ba ta kawar da shi daga mulki ba.
R

No comments:

Post a Comment