Sunday, 19 August 2018

Gwamna Ganduje ya jagoranci rabawa matasa 8,800 tallafin Naira 20,000 kowanensu

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR Ya Jagoranci Taron Bada Tallafin Kudi Naira dubu Ashirin 20,000 Ga Matasa dubu Takwas sa dari takwas 8,800 dasuka fito daga fadin Kananan Hukumomi Na Jihar Kano a Fadar Gwamnatin Jihar Kano. 


Wannan yana daya daga cikin shirin Gwamnati na samawa matasa Sana'ar dogaro dakai kamar yadda Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari take gabatarwa. 

A Jawabinsa Mai Girma ya bayyana cewar Gwamnatinsa zata cigaba da irin wannan Tallafin fa Matasa a Jihar Kano kamar yadda takeyi a baya inda yabada tabbacin makamacin wannan taron na Mata shima zaayi a Yau dinnan. 

Tunda Farko Kwamishinan Kananan Hukumomi Na Jihar Kano Alh Murtala Sule Garo ya bayyana cewar an dakko matasa 200 ne daga Kowacce Karamar Hukumar Mata kuma 150 daga kowacce Karamar Hukuma.

Abubakar Aminu Ibrahim 
SSA Social Media II,Kano.b

No comments:

Post a Comment