Sunday, 19 August 2018

Gwamnan da ya koma PDP bayan fita daga APC na shirin tsallakawa SDP

Rahoton da muka samo daga Benue News na nuni da cewar akwai yiwuwar Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue yana shirye-shiryen ficewa daga PDP zuwa SDP bayan masu neman takarar gwamna 12 da ke jihar sun cimma matsayar cewa dole sai anyi zaben fidda gwani.


Idan ba'a manta ba a baya, manema labarai sun ruwaito cewa 'yan takarar kujerar gwamna a jihar sun ki amincewa a bawa gwammna mai ci tikitin takarar kai tsaye.

Wannan na faruwa ne wata daya bayan gwamna Ortom ya fice daga jam'iyyar APC sakamakon 'jan katin' da yace shugabanin jam'iyyar na jiha sun bashi.

Tun bayan dawowarsa jam'iyyar na PDP, gwamna Ortom ya yi kokarin sauya tsarin jam'iyyar a jihar saboda ya samu ikon juya jam'iyyar yadda yake so amma 'yan jam'iyyar ciki har da tsohon gwamnan jihar Gabriel Suswan sunki amincewa da hakan.

Wannan takadamar ta janyo shugabanin PDP karkashin jagorancin Uche Secondus ta kafa kwamiti domin wareware matsalar kuma bisa dukkan alamu kwamitin tafi son a bawa Ortom tikitin takarar gwamna a jihar amma sauran 'yan takarar gwamna a jihar sunki amincewa da hakan.

Saboda wannan matsayar da 'yan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP a jihar ne yasa Ortom ya fara tunanin komawa jam'iyyar SDP inda akace ya yi alkawarin bawa jam'iyyar makuden kudi a matsayin tallafi domin su bashi tikitin takarar gwmna.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment