Tuesday, 7 August 2018

Gwamnati Ta Yi Allah Wadai Kan Yadda Jami'an DSS Suka Mamaye Majalisa

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo Ya Yi Allah Wadai Bisa Yadda Jami'an tsaro na farin kaya wato, DSS Suka mamaye Majalisar tarayya ba bisa umarni ba.


Osibanjo ya bayyana matakin mamaye majalisar a matsayin abin da ya saba tsarin mulki da na doka inda ya bayar da tabbacin hukunta duk wanda ke da hannu cikin lamarin.

Wata majiyar jaridar " Sahara Reporter" ta yi nuni da cewa Shugaba Buhari ne ya bayar da umarnin sallamar Shugaban Rundunar DSS bisa zargin cewa yana yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki aiki ne kuma jami'ansa sun mamaye harabar majalisar tarayya ce don kunyata Buhari.
Rariya.

No comments:

Post a Comment