Sunday, 12 August 2018

Gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyin karatun dalibar da ta samu sakamako mafi kyau daga jami'ar UDUS

Uwargidan gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Bagudu ta shiryawa matasa su 45 'yan asalin jihar da suka kammala karatun aikin likita daga jami'o'i daban-daban ciki hadda na kasashen waje liyafa inda har aka karramasu.
Kowannensu an bashi na'ura me kwawalwa kamar yanda me magana da yawunta ta bayyana amma akwai daliba daya da ta yi zarra me suna, Asama'u Bello, ta kasance dalibar da ta kammala karatu da sakamako mafi kyau tsakanin dalibai daga jami'ar UDUS dake jihar Sakkwato.

Wannan dalili yasa gwamnatin jihar Kebbin ta dauki nauyin karatunta zuwa duk wata jami'ar da take da burin zuwa da kuma irin karatu da take son yi.

Muna musu fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment