Friday, 17 August 2018

HAJJIN BANA: Alhazai Sun Saurari Huduba Mai Ratsa Jiki

Alhazai a birnin Makka,  a yau jumma'a sun saurari huduba mai ratsa jiki da gamsarwa daga bakin daya daga cikin manyan limaman Harami,  Sheikh Sa'ud Al-Shuraim akan girma da falalan aikin hajji. 


Akalla mutane miliyan biyu ne daga kowani sassa na duniya suka halarci kasa mai tsarki don gabatar da ibadan aikin Hajji. 

Mahajjatan zasu nufi Mina don fara aikin hajjin a ranar lahadi inda daga nan zasu wuce Arafa a ranar Litinin don gudanar da babban ibada na aikin hajjin.

Hukumomin Saudiyya suna haba haba da alhazai don ganin sun gababatar da ibada yanda ya dace. 

Hukumar Hajji da Umra na kasar sun samar da numba na musamman don taimakawa mahajjata,  yayin da ministan,  Mohammed Saleh Banten yace aikin Hajji da siyasa basu da mahada. 

Ya ce kasar Saudiyya ba za ta dora wa musulmai wani sharadi ba a yayin aikin hajji. 

A wani taron manema labarai,  shugaban hukumar fasfo na Saudiyya yace zuwa yanzu mahajjata 1, 684, 629 ne suka halarci kasa mai tsarki don ibadan aikin Hajji.
rariya.

No comments:

Post a Comment