Monday, 20 August 2018

Hajjin Bana: Yau za'a canja rigar Ka'aba

Bayan shirye-shiryen cire tsohuwar rigar ka'aba da akayi jiya, Lahadi, a yau, Litininne, Ranar Arafa za'a canjawa Ka'aba sabuqar riga.


Duk shekara ana cire rigar sannan a maye gurbinta da sabo ranar tara ga watan Dhu Al-Hijjah, wanda ya yi daidai a ranar Litinin 20 ga watan Agusta na wannan shekarar.

Ana kiran rigar da suna "Kiswa" a Larabce - kuma launinta baki ne tare da ratsin ruwan gwal.


Muna fatan Allah ya amsa ibadun Alhazanmu.No comments:

Post a Comment