Saturday, 18 August 2018

HAJJIN BANA: Hukumar NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya 37,746 Zuwa Kasa Mai Tsarki

Hukumar Kula da Harkoki da Jin dadin Alhazai ta Najeriya, NAHCON ta samu nasarar kammala jigilar alhazai 37,746 cikin sawun jiragen sama sau 90 daga Najeriya zuwa kasar Saudi Arabia domin gabatar da Hajjin bana. Sanarwan hakan ya fito ne daga sashin lura da karbar kwaman a karkashin hukumar ta NAHCON a jumu'ar data gabata. 


Wannan sashi da aka ambata shike lura da kididdiga da yada tashin jiragen sama dake  jigilar alhazan daga kowanne filin tashin jiragen sama a Najeriya. Jigilar kwashe alhazan dai ya gudana ne da kwangilar sanannun kampanonin jiragen sama dake Najeriya: MaxAir, MedView tare da goyon bayan sanannen kampanin jirgin sama mallakar kasar Saudi Arabia wato Flynas Air. An karkare jigilar kwasan alhazan daga Najeriya a ranar Juma'ar da ta gabata.

Bayaga jimillar alhazan da ake kaiwa Saudi Arabia daga jahohi 36 daga Najeriya da babban birnin tarayya, Abuja harma da na Rundunar Sojoji, akwai wasu alhazan Kuma da Basu kasa 20,000 ba wadanda ke tafiyarsu ta hanyar jiragen yawo mallakar kampanoni masu zaman kansu.

Shide aikin hajjin na bana zai kankama ne daga ranar Lahadi Mai zuwa da izinin Allah. Ana sa ran alhazai sama da miliyan 2 ne zasu gabatar da wannan muhimmin aiki Kuma a ranar zasu Yi dandazo a farfajiyar muna. Alhazan zasu zarce farfajiyar Arafat a ranar litinin inda ake sa ran zasu wuni suna zikirori da ibada yayin da zasuyi addu'o'i domin neman yardar Allah DA gafarar sa. Daga bisani Kuma alhazan zasu zarce zuwa Muzdalifa a cikin manyan motocin da aka tanada. A Muzdalifa, Wanda ke tsakanin Arafat da Muna  ne alhazan su miliyan 2 zasu kwana har zuwa washe gari talata domin su wuce jifan shaidan karo na farko a Jamaraat. 

Mal. Aliyu Tanko, Jami'in kula da inganci, tantancewa da tabbatar da dabbaka tsare tsaren hukumar alhazan yace za'a gudanar da jifan shaidan din ne a kan tsarin daki-daki, gungu-gungu. 

Mal. Tanko Wanda tun wuri yaje Muna domin ran gaadi da tantance kayan Jin dadin alhazan Najeriya, ya Karin haske ga manema labaru cewa "duk alhazai zasu dawo tantunansu ne bayan su kammala zamansu na Muzdalifa. A tantunansu ne zasu jira lokutan da aka ware musu bisa ga tsarin da akayi na gungu-gungu, sahu-sahu tareda jami'an da zasu taimakamusu domin zuwa jamaraat..." 

A hajjin shekarar 2015 ne aka samu turmutsu-tsi mai tada hankali Kuma a sanadiyyar hakan akayi rashin dumbin alhazai wasu daga Najeriya. Tun daga wannan lokaci ne hukumar Saudi Arabia ta dabbaka wannan tsari na zuwa jifa a sahu-sahu, kuma lokaci-lokaci domin gujewa sake afkuwar wata larurar Mai kamada waccar.
Rariya.

No comments:

Post a Comment