Wednesday, 29 August 2018

Har Yanzu Jihar Kano Ba Ta Da Mataimakin Gwamna

A ranar 4 ga wannan wata na Augusta ne tsohon mataimakin gwamnan Kano Farfes Hafizu Abubakar, ya mika takardar sauka daga kujerar sa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje.


Yanzu haka dai ‘yan siyasa da dama na ci gaba da zawarcin wannan kujera ta mataimakin gwamnan wanda hakan dai na zuwa ne kasa da shekara guda da ya rage wa’adin shekaru 4 na gwamnatin jihar Kano ta Abdullahi Umar Ganduje, ya kammala, to amma har ya zuwa wannan lokaci, gwamna Abdullahi Umar Ganduje,bai fitar da wanda zai gaji farfesan ba.

Yanzu haka dai masana harkokin dokokin kasa da shari’a na ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da wanann batu, kamar yadda zakuji a cikin wannan rahoto da Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana daga Kano.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment