Thursday, 2 August 2018

Har Yanzu Sakkwatawa Na Tare Da Buhari Dari-bisa-dari>> Sanata Wamakko

Sanata Wamakko ya bayyana cewa, a ranar Asabar za a ga wanda ke da jama'ar Sokoto. Kuma ya bayyana cewa jama'ar Sokoto duka sai wasu 'yan kadan ne basa tare da Buhari amma Sokoto ta Buhari ce da jam'iyyar APC.


Sanata Wamakko ya kara da bayyana cewa da iznin Allah ranar Asabar zai shiga Sokoto kuma za a tabbatar da jihar Sokoto ta Buhari da APC ce.

Haka kuma ya bayyana fitar wasu a jam'iyyar APC ba wani abin damuwa bane ko kadan domin har gobe talakawa na tare da Buhari da jam'iyyar APC.
rariya.

No comments:

Post a Comment