Sunday, 19 August 2018

Hazard ya kawo karshen rade-radin komawa Madrid, yace yana nan daram a Chelsea

Tauraron dan kwallon Chelsea,  Eden Hazard ya kawo karshen rade-radin da akeyi na cewa zai koma Real Madrid, tun bayan tafiyar Cristiano Ronaldo daga Madrid ake alakanta Hazard da zuwa Madrid din dan maye Ronaldo, a yayin da aka rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a Ingila, ta Sifaniya tana nan a bude.


Bayan kammala wasansu da Arsenal a ajiya wanda ya kare Chelsea na lallasa Arsenal din da ci 3-2, Hazard ya bayyanawa RMC Sport cewa, yana nan a Chelsea babu inda zashi.

Har yanzu yana da sauran shekaru 2 a Chelsean kamin kwantirakin daya sakawa hannu ya kare sannan a Ingila an kulle kasuwar cinikin 'yan wasa wanda hakan na nufin kungiya zata iya sayar da dan wasa amma ita ba zata sayo ba.

Ya kara da cewa, to baya tunanin Chelsea zasu iya sayar dashi tunda ba zasu samu madadinshi ba a yanzu.

Yace, masoyan kungiyar suna sonshi kuma shima yana jin dadin zamanshi a kungiyar amma dai zuwa nan da shekara me zuwa ko kuma shekaru biyu masu zuwa zamu ga abinda zai faru.

No comments:

Post a Comment