Tuesday, 28 August 2018

HUKUNCIN JIFAN SHUGABANNI DA YI MUSU ATURE>>Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

MUSULUNCI YA BAYYANA HAKKIN SHUGABANNI DA MABIYA, YA KUMA FADI YADDA MUAMALA ZATA KASANCE DA KOWA, 


BAYA DAGA CIKIN KOYARWA TA ADDINI CIN MUTUNCIN SHUGABANNI,  DA JIFAR SU,  DAYI MUSU IHU DA ATURE, DA WASU  ALUMMA SUKEYI, WANNAN YA SABAWA KOYARWAR ADDINI, DA KYAKYAWAR AL'ADARMU, DA MUTINCINMU DA HALAYANMU MASU KYAU.

IDAN SHUGABA BAYI MAKA ABINDA KAKESO BA ,KAYI AMFANI DA DAMAR KA DA AKA BAKA WAJAN ZABE IDAN YA ZO KA CANJA  SHI DA WANDA KAKE GANIN YA FISHI.

KU KUMA SHUGANNI YA KAMATA KU SANI LOKACI YA CANJA KAN TALAKAWA YA WAYE,  ALKAWURAN KARYA,  DA KARYA DA YAUDARA, DA  CIN DUKIYAR TALAKAWA DA WAWURA DA RIF DA CIKI DA HAMDUMA DA  BABA KERE , YA WUCE .

YANZU KO  KAYI DA GASKE KO KA HAKURA DAYIN TAKARA ,  AMMA MULKI SAI KA SHIRYA. 

ALLAH YA BAMU SHUGABANNI NA GARI YA BAMU LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA.

No comments:

Post a Comment