Sunday, 12 August 2018

In da Ranka: Za a samar da barasa daga al'aurar mata

Kasar Poland ta sanar da cewa za ta fara sayar da wani samfurin barasa wacce aka samar da ita daga wani sinadirin al'aurar mata.


Sunan mutumin da a yanzu haka duniya ke ci gaba da jinjana wa game da wannan sabuwar fasahar shi ne, Wojciech Mann.

Mann, ya amsa tambayoyi kan yadda wannan tunanin ya gitto masa, kamar haka:

"Wannan tunanin ya zo mun ne shekaru shida zuwa bakwai da suka shude, a lokacin da na ke kwankwadar giya a wani gidan shan barasa na kasar Beljiyom.A lokacin na dinka tambayar kaina, shin ko me yasa barasa ke da tsami?.Bayan na zurfafa bincike a yanar gizo, sai na gano cewa musabbin wannan lamarin shi ne, rashin sinadirin kwayar halittar lactic acid,wacce ake samun ta a al'aurar mata.A lokacin da na gane hakan,sai na kwala ihu me tsanani, na ji dadi.Nan take na gano mu'alamar da ke tsakanin mata da barasa.Wannan shi ne ainahin takaitaccen labarin wannan sabuwar giyar".

Haka zalika ya kara cewa, "Tuni kwastamomi daga sassa daban-daban na duniya ke ci gaba da yin odar barasar kafin ma mu fara kai ta kasuwa.Alal misali mutanen Amurka,Latin Amurka,Gabashin Turai,wasu sassan Rasha da kuma kasar Iskandinaviya na ci gaba da neman ganawa da mu ta wayar tarho.Shi yasa na yi imani cewa, zamu yi matukar arziki.Za mu yi amfani da sinadirin lactic Acid wanda muka samu daga al'aurar mata.Ko shakka babu wannan sabon abu ne.Wannan sinadirin daya yake da kowane irin sinadiran da za a iya amfani da shi a yogot,salad da sauran na'au'o'in abinci.A yanzu za a fara sayar da barasar a kasar Poland kawai,inda daga bisani za mu sayar da shi a kasuwannin fadin duniya".
TRThausa.

No comments:

Post a Comment