Friday, 3 August 2018

Ina da dakin da ba kowa>>Mansurah Isah

A wani yanayi na nuna soyayya da shakuwar dake tsakaninta da mijinta, tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa wadda yanzu ta koma tallafawa gajiyayyu, Matar Sani Musa Danja, Watau Mansurah Isah ta yiwa mijin nata kirari da ya dauki hankulan mutane.Mansurah ta bayyana cewa, Mai buhu buhu, angon Mansurah mai komai dozen mai babban riga. Bakin rai bakin fama. Ni uwar gidace, dole a kwashi gaisuwa a wajen mama.

Ta kara da cewa, tana da dakin da ba kowa.
Lamarin ya dauki hankulan mutane inda da dama su ka ta sha'awar irin soyayyar Mansurah da mijinta, Sani Danja kuma suka yi musu fatan Alheri.

Muna fatan Allah ya kara dankon soyayya.

No comments:

Post a Comment