Thursday, 16 August 2018

Jama'a Buhari fa bashi da lafiya, Wasu ne ke juya kasarnan ba shiba: Ni kuma gashi anata huromin wuta har daga kasashen waje sai na tsaya takarar shugaban kasa>>Gwamna Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal wanda yana daya daga cikin wadanda suka canja sheka kwanannan daga jam'iyya me mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari fa bashi da lafiya, wasune kawai dake kewa dashi ke gudanar da al-amuran kasarnan amma ba shiba.


Ya kara da cewa, wasune masu son cimma burin su kawai ke gudanar da al'amuran kasarnan amma ba Buhari ba, yace, a shekarar 2015 sun goyi bayan shugaba Buhari saboda gaskiyarshi amma fa a sani cewa, ba gaskiyar mutum bace kawai ke sa ya zama shugaba na gari ba.

Tambuwal yayi wannan maganne a likacin da wasu kungiyar dalibai suka kaimai ziyarar godiya bisa baiwa matasa muhimmanci da yayi a mulkinshi.

Tambuwal ya kara da cewa, shi kam a yanzu bashi da sakat, domin kuwa jama'a a ciki da wajan kasarnan sun huromai wuta akan cewa sai fa ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Gambuwal yace, kwanannan wani ya kirashi da cewa shi yarone, to hakan a gareshi yabone domin an sakashi cikin matasan da zasu iya kawo canji da cigaba a kasarnan, kamar yanda jarudar Punch ta ruwaito.

1 comment: