Sunday, 19 August 2018

Jarumin fina-finan Hausa, Ayuba Dahiru, Tandu ya rasu

Da safiyarnanne muke samun labarin rasuwar jarumin fina-finan Hausa, Ayuba Dahiru wanda akafi sani da Tandu, jarumin da yafi karfi wajan yin fina-finan barkwanci,ya rasune bayan gajeruwar rashin lafiya ta kwana biyu.


Daya daga cikin abokan aikinshi, Falalu A. Dorayine ya bayyana haka a dandalinshi na sada zumunta.

Ga abinda ya rubuta kamar haka:

"Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un
Allah yaiwa Jarumin barkwanci AYUBA DAHIRU (TANDU) rasuwa.
Ya rasu Yau Lahadi 19/8/2018
Bayan gajeriyar rashin lafiya ta kwana biyu. 
Allah ya jikansa yai masa rahma
Allah yasa mu cika da Imani."

Muna fatan Allah ya kai rahama kabarinshi ya kuma Albarkaci abinda ya bari.

No comments:

Post a Comment