Saturday, 4 August 2018

Jihohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari ya lashe a zaben 2019

Yayin da shekarar zabe ta 2019 ke ta kara matsowa, masana harkokin siyasa da ma masu fashin baki akan al'amurra na ganin cewa har yanzu fa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke kan gaba wajen farin jini a al'ummar kasar.


Hakan dai kamar yadda suka bayyana za'a iya ganewa idan aka yi duba na tsanaki a tsakanin kafatanin jahohin Najeriya aka kuma dora su akan sikelin wadanda zai iya lashewa da kuma faduwa a zaben mai zuwa.

Duk da dai har yanzu jam'iyyar adawa ta PDP bata fitar da nata dan takarar ba, amma dai ana hasashen cewa shugaba Buhari zai iya lashe akalla jahohi 21 a zaben mai zuwa. Idan kuma aka hada da babban birnin tarayya, to a iya cewa ma jahohi 22.

Ga dai su kamar haka:

1. Adamawa

2. Bauchi

3. Borno

4. Ekiti

5. Gombe

6. Jigawa

7. Kaduna

8. Kano

9. Katsina

10. Kebbi

11. Kogi

12. Lagos

13. Nasarawa

14. Niger

15. Ogun

16. Ondo

17. Osun

18. Oyo

19. Sokoto

20. Taraba

21. Zamfara

22. Sai kuma babban birnin tarayya Abuja

No comments:

Post a Comment