Sunday, 26 August 2018

Juventus ta buga wasanta na biyu amma har yanzu Ronaldo be ci mata kwalloba: An sokeshi saboda nuna rashin jin dadin cin kwallon abokin wasanshi

A karo na biyu da Cristiano Ronaldo ya bugawa sabuwar kungiyarshi ta Juventus wasan gasar Serie A har yanzu dai bai samu yaci mata kwallo ko guda ba, wasan da Juve ta buga da Lazio jiya, Asabar, ya kare Juven nacin 2-0.


Saidai hankula sun karkata kan Ronaldo inda ake ta tsammanin zaici kwallo amma hakan bata samu ba.

Ronaldo ne dai ya zama gwarzon dan kwallon da yafi nuna bajinta a wasan na jiya amma nuna rashin jin dadin da yayi kan kwallon da abokin wasanshi, Mario Mandzukic yaci ta jawo mai surutai da Allah wadai.

Ronaldon dai yaje cin kwallo amma sai ya barar da damar , nan take Mandzukic ya samu kwallon ya kuma sakata a raga. Cin wannan kwallon ke da wuya sai Ronaldo ya ya motse fuska ya watsa hannu sama, alamar jin haushi kenan, amma daga baya yayi murmushin karfin hali.
Wannan abu da Ronaldo yayi yasa masoya kwallo da dama, musamman magoya bayan abokin takararshi, watau Messi suka rika sukarshi a shafukan sada zumunta inda sukace ya cika son kanshi da yawa da kuma nuna a koda yaushe shi yake so yayi abin gwaninta.

Saidai me horas da 'yan kwallon Juve, Massimiliano Allegri ya kare Ronaldon inda yace dan wasan yayi kokari kuma salon wasan Juve dana Madrid ba daya bane dan haka har yanzu Ronaldon na kara fahimtar salon wasan kungiyarne, ya kuma ce bawai fushi Ronaldo yayi ba kawai dai irin abinda ya saba faruwane.

Ya kuma ce yaji dadin yanda sakamakon wasan ya kare, kamar yanda ya gayawa Sky Sport.

Wasa na gaba da Juve zata buga ranar 1 ga watan Satumba tsakaninta na kungiyar Parma ne, abin jira a gani shine ko Ronaldon zai ci kwallo a wasan na gaba?

No comments:

Post a Comment