Saturday, 18 August 2018

Juventus tayi nasara a wasanta na farko amma Ronaldo be ci mata kwallo ba

A yau, Asabar, 18 ga watan Augusta 2018, Juventus ta buga wasanta na farko a gasar Serie A tare da kungiyar Chievo, Juve tayi nasara a wasan da sakamon 3-2 amma kuma sabon dan wasanta da ta sayo daga Real Madrid, Cristiano  Ronaldo, be ci mata kwallo ba.


Dubban maso ya kwallon kafa ne suka kalli wasan da fatan cewa Ronaldon zai ci kwallo, har tsohon dan kwallonnan Pele sai da ya aikewa da Ronaldo sako ta Twitter inda ya mishi fatan samun sa'a a wasan.

Duk da yakai hare-hare da shata-shatai amma be samu saka kwallo ko daya ba, har bugun fenaret yaso samu amma sai alkalin wasa yace ba fenaret bane.

Masu sharhi dai na ganin cewa, Ronaldon zai dan dauki lokaci kamin ya warware ya fara irin wasan da ake tsammin ganin yayi tunda har yanzu be gama sabawa da yanayin wasan kungiyar ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Chievo nada wahalar buga wasa ga abokan hamayya kuma albashin Ronaldo kawai ya nunka na gaba dayan 'yan wasan Chievu din sau uku.

No comments:

Post a Comment