Friday, 24 August 2018

Juventus zata ajiye Ronaldo a benci a wasanta na gaba

Tauraron dan kwallon kafa Cristiano Ronaldo dake bugawa Juventus wasa zai iya yin zaman benci a wasan kungiyar na gaba kamar yanda me horas da 'yan wasa na kungiyar, Massimiliano Allegri ya bayyana, yau Juma'a.


Massimiliano Allegri ya gayawa manema labarai cewa, yanzu Ronaldo zai iya buga wasa amma zai yi zaman rabin awa a benchi kamin a sakashi fili, wannan na zuwane kwana daya kamin wasan da Juve zata buga da Lazio gobe, Asabar.

Kocin ya kara da cewa, irin haka ya faru da Ronaldo lokacin yana Real Madrid, kamar yanda ANSA ta ruwaito

No comments:

Post a Comment