Wednesday, 8 August 2018

'Kadan ya hana 'yan bangar da Saraki ya kai majalisa su kashe wani dan APC'

Wata sanarwar da mukaddashin kakakin jam'iyyar, Yekini Nabena, ya fitar ta ce binciken da jam'iyyar ta gudanar ya gano cewar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya shirya tayar da hankali domin hana yunkurin tsige shi.


Ta kuma ce da ba don jami'an tsaro ba, da an yi tashin hankali da ka iya haddasa salwantar rayuka a majalisar.

Sai dai kuma Saraki ya ce babu hujjar kai jami'an tsaro majalisar dokokin kasar domin su musguna wa 'yan majalisa.

A sanarwar da APC din ta fitar ranar Laraba, ta yi zargin cewar Saraki ya kai 'yan bangar siyasa majalisar kuma saura kiris 'yan bangar su kashe dan majalisar wakilai na APC daya tilo da ya je majalisar, E.J. Agbonayinma, da ba don taimakon jami'an tsaro ba.

Jam'iyyar ta kuma nemi sanin dalilin da ya sa shugaban majalisar dattawa ya kira taron 'yan majalisa domin dakile yunkurin wasu 'yan majalisa na tsige shi.

Ta kuma ce abin mamaki ne cewar 'yan majalisar jam'iyyar PDP ne kawai suka je majalisar tun karfe bakwai na safe, yayin da 'yan majalisar APC ke zama game da halin da kasa ke ciki a wani wuri daban.

Jam'iyyar ta nemi hukumomi su yi bincike kan abubuwan da ta gano tare da kira ga Saraki ya sauka daga kujerar shugaban majalisar dattawan nan take.

An jima ranar Laraba ne dai Saraki din zai gabatar da jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin kasar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment