Wednesday, 8 August 2018

Kalli dandanzon jama'ar da suka taru a jihar Akwa-Ibom wajan komawar Sanata Akpabio APC

A yau, Larabane, tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom, Sanata Godswill Akpabio yayi taro a jihar tashi inda ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar APC, dandazon masoyanshine suka taru dan nuna goyon baya a gareshi.Kamin wannan lokaci dai, Sanata Akpabio wanda shine shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, ya ajiye mukamin nashi sannan ya kaiwa shugaba Buhari ziyara a Landan inda yake hutu, bayan nan kuma ya gana da jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu.


No comments:

Post a Comment