Friday, 17 August 2018

Kalli igiyar daure takalmi da ake sayarwa akan kudi sama da miliyan 2

Masu iya magana sukace, Duniya gidan kashe ahu..., wani abune da ya dauki hankulan mutane sosai da dama suka rika bude baki cikin mamaki da ganinshi, wai irin abin daure takalminnanne da ake ganin hotonshi a sama ake sayar dashi akan kudi sama da naira miliyan biyu.Abin daure takalmin dai na shahararren kamfanin sayar da kayannan ne masu tsada wanda dama sai wadanda suka rufa suka tada kai ke sa kayan da ya kera me suna GUCCI.

Lamarin ya dauki hankulan mutane a shafukan sada zumunta inda akaita mamakin wannan uwayen kudi tsagwagwa haka akan wannan abu da wasu sukace  dari zuwa dari biyu suke sayenshi a kasuwannin Najeriya.

No comments:

Post a Comment