Monday, 6 August 2018

Kalli yanda wani limami yaci gaba da jan Sallah yayin da ake girgizar kasa a kasar Indonesia

Tabbas Imani matsayi-matsayi ne sannan kuma duk wanda ya dogara ga Allah to ya isar masa, wannan Limamin da bidiyonshi yayi ta yawo a shafukan sada zumunta da muhawara yasha yabo daga wajan musulmai da wadanda ba musulmaiba.


A yayin da yake jagorantar Sallah a kasar Indonesia aka fara girgizar kasa, da yawa daga cikin mamu dake bayanshi sun tsere amma shi Allah ya saka mishi nutsuwa ya ci gaba da sallah, tabbas wannan abu akwai taba zuciya. 

Ya zuwa yanzu mutane 98 ne aka tabbatar sun mutu a wannan girgizar kasa da ta auku.

Muna fatan Allah ya jikan musulmai yasa kaffarane.

Kalli bidiyon anan kasa:

No comments:

Post a Comment