Saturday, 4 August 2018

Karanta dalilin da ake tunanin yasa masu garkuwa da mutane sace Sheikh Al-Garkawi

Labarin garkuwa da shahararren malamin addinin Islama dake garin Kaduna, Shiekh Ahmad Adam Algarkawi ya kada jama'ar jihar dama sauran jihohin Arewa da dama, malamin yayi suna wajan kokarinshi na nuna halayyar Zuhudu, watau gudun Duniya.


Akwai Asibiti da Makaranta da masallaci dake karkashin kulawar malamin.

Dabi'ar malamin takan birge dukkan musulmi na kwarai, labarai da dama da ake bayarwa akan malam na irin yanda yake yawo akan keke da kuma wasu lokuta ko da a mota za'a daukeshi yakan kin yarda( saboda be san ta yanda aka samu kudin sayan motarba, kamar yanda da dama ke fassarawa).

Bayan yin garkuwa da malam a ranar Alhamis din data gabata, jama'a sun rika danganta haka da cewa, makudan kudin da malamin ya gada daga gurin wani dalibinshi daya rasu ne suka sa aka saceshi.

Labarin na cewa, akwai wani kasaitaccen attajiri wanda dalibin Sheikh Algarkawine, kamin ya rasu, ya bar wasiyya cewa, idan ta Allah ta faru gareshi, to a raba dukiyarshi gida uku a baiwa malam kashi daya.

Jama'ar gari sun rika fassara kudin da malamin ya gada da miliyoyi darurra kai wasu ma sunce sunfi haka.

Daya daga cikin na hannun damar Sheikh Algarkawi ya bayyanawa shafin hutudole.com cewa, tabbas wancan labari na gado akwaishi, amma abinda ya kamata mutane su gane, shine ba fa wai tsabar kudi ne aka bayar ba, a'a kadarorine, da suka hada da filaye da gidaje.

Da aka tambayi malamin shin zai iya kiyasta darajar wadannan kadarori sai yace, a'a.

Sannan ya kara da cewa, ba Shiekh Algarkawi aka baiwa gadon yayi amfani da shi a karon kanshi ba, an bayarne dan ci gaban madallaci da makaranta.

Da aka tambayeshi ko wannan gado da aka bayar yana da alaka da sace Sheikh Algarkawi?, sai yace, wannan shaci fadine na mutane amma su dai basu sani ba.

Saidai malamin yaki cewa uffan akan maganar yanda ake ciki game da sace Sheikh Algarkawin inda yace basa so a watsa Duniya ta sani.

Andai sace malamin tare da wasu dalibanshi da sukaje zagayen gona.

Muna fatan Allah ya bayyanashi da daliban nashi cikin koshin lafiya.

No comments:

Post a Comment