Tuesday, 28 August 2018

Karanta ka karu: Yanda aka samo asalin kalmar bindiga

A yayin da akayi ranar Hausa a shafukan sada zumunta da muhawara, wani bawan Allah ya bayar da labarin yanda kalmar Bindiga ta samo Asali.Mutumin yace inda aka samo asalin kalmar bindiga shine a lokacin turawan mulkin mallaka sukan tafi farauta da masu rike musu bindiga, idan suka hangi dabbar da suke so su harba sai su cewa me rike da bindigar, bring the gun, wai shi kuma da ke ba turanci yake ji ba sai yaji kamar ance Bindiga.

Mutumin ya kara da cewa wani farfesa ne a jami'ar Bayero ta Kano ya gaya haka.


No comments:

Post a Comment