Saturday, 4 August 2018

Karanta labarin sarkin Yarbawan da yace yafi Dangote kudi

Wani basaraken gargajiya a yankin Yarbawa watau Oluwo of Iwo land, Oba AbdulRasheed Adewale Akanbi ya fito ya bayyanawa duniya tarin dukiyar sa da kadarorin sa da yake da su.


Haka ma Sarkin yayi ikirarin cewa a duk Najeriya babu mahalukin da ya kai shi kudi ciki kuwa hadda fitaccen mai kudin nan na Najeriya da ma nahiyar afrika baki daya, Alhaji Aliko Dangote.

Sarkin ya zayyana dukkan kadarorin dake a cikin kasar sa a matsayin nashi ciki kuwa hadda na kamfanin Dangote da ma dukkan al'ummar kasar ta sa.

No comments:

Post a Comment