Wednesday, 8 August 2018

Karanta labarin yanda jami'an DSS sukayi farin ciki da korar da akawa Lawal Daura

Jami’an Hukumar tsaro ta DSS masu fararen kaya sun yi farin ciki da jin labarin cewa Mukaddashin Shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki jiya.


Majiyar mu ta bayyana mana cewa an barke da murna da shewa a sa’ilin da labari ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ke rike da kasar na rikon kwarya ya kori Shugaban Hukumar DSS Lawal Daura daga ofis.

Har a Hedikwatar DSS wanda ake kira Yello House, Ma’aikata sun yi farin cikin jin cewa an sallami Shugaban na su daga aiki. A 2015 ne Shugaba Buhari ya dawo da Lawal Daura ofis ya rike DSS bayan an yi masa ritaya a baya.

Jami’an tsaron da aka aika su tare Majalisar kasar jiya ma sun ji dadin jin labarin cewa Lawal Daura ya bar ofis. An dai soki abin ya auku jiya a Majalisar kasar wanda yayi sanadiyyar korar Daura daga aiki.

No comments:

Post a Comment