Sunday, 12 August 2018

Karanta labarin yanda Obasanjo ya rika lalata da mata yana basu rijiyar mai lokacin yana mulki

Sanannen marubucin Najeriyarnan, farfesa Wole Soyinka ya caccaki tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo inda ya zargeshi da cewa, lokacin yana shugaban kasa ya rika lalata da mata yana basu rijiyoyin mai.


A cikin wani littafi daya rubuta, Soyinka yace, yasan Obasanjo shima kuma ya sanshi, baya magana babu hujja, yana kalubalantarshi daya fito ya rantsewa 'yan Najeriya cewa be taba yin lalata da mata ya basu rijiyar mai ba lokacin yana shugaban kasa. Ya kuma jawo hankalin Obasanjon da ya lura da yanda yake gudanar da rayuwarshi ganin cewa kullun rana ta  Allah yana jara kusantar mahaliccinshine da kuma ranar sakamako.

Ya kara da cewa Obasanjon makaryacine na intaha inda yace, shuwagabannin kasar Amurka biyu, Bill Clinton da Donald Trump an zargesu da yin lalata da mata inda suka basu wani abu amma yace ba'a taba zarginsu da yin lalata da mata ba suka basu kyautar wani abin da ya shafi kwangila ko kuma dukiyar kasa ba.

Ya kara da cewa, a lokacin mulkin Obasanjone aka rufe wani zababben gwamna a bandaki inda aka tilasta mishi saka hannu akan wani cek dan fitar da wasu makudan kudi daga asusun jiharshi.

An kaddamar da wannan littafine a birnin Legas kamar yanda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN suka ruwaito.

Farfesa Wole Soyinka dai ya shahara wajan sukar tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo inda ya kuma zargeshi da toshe mai hanyar samun mukamin sakataren majalisar dinkin Duniya.

No comments:

Post a Comment