Friday, 3 August 2018

Karanta yanda wani dan Najeriya ya cikawa wannan baturen Alkawari ya aikamai da rigar 'yan kwallo kasar Amurka

A lokacin gasar cin kofin Duniya 2018 da aka buga a Rasha, rigar 'yan kwallon Najeriya ta dauki hankulan masoya kwallo daga sassan Duniya daban-daban inda a ranar da aka fara sayar da ita a Ingila ta kare karkaf.Haka kuma duk da irin wasu labarai marasa dadi da wasu lokutan akan danganta Najeriyar dashi, har yanzu akwai na gari masu jawo mata farin jini a idon Duniya.

Wannan wani baturen kasar Amurkane daya bayar da labarin cewa, ya hadu da wani dan Najeriya a kasar Rasha wajan buga gasar cin kofin Duniya 2018, ya kuma bashi labarin irin yanda yake son rigar 'yan kwallon Najeriyar amma gashi ta kare, yanzu babu inda zai samu ya siya.

Mutumin me suna Greg Dybec yace dan Najeriyar ya amshi adireshin shi ya kuma mai alkawarin cewa zai aikamai da rigar 'yan kwallon.

Yace kawai dai ya jishine a wancan lokacin amma sai gashi yau yaga rigar an aiko mishi ita daga Najeriya, ya karkare labarinshi da cewa har yanzu akwai mutanen kirki masu taimakon wadanda basu sani ba.

Wannan labari nashi, kamar yanda ya bayar dashi a shafinshi na twitter yayi matukar daukar hankulan mutane.

No comments:

Post a Comment