Tuesday, 21 August 2018

'Kasar Amurka ta caccaki gwamnatin Shugaba Buhari kan Kashe-Kashe

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, 'kasar Amurka ta na zargin aukuwar kashe-kashe musamman a yankunan Arewa na Najeriya a sanadiyar rikon sakainar kashi da nuna halin ko oho.


Gwamnatin 'kasar Amurka ta bayyana cewa, ci gaba da aukuwar kashe-kashe a kasar nan ya bayu ne a sakamkon rashin daukan matakai gami da rashin tsauraran hukuci daga bangaren gwamnati.

Wani shugaba na ofishin jakadacin kasar Amurka dake Najeriya, David Young, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Jos dake jihar Filato a daren ranar Lahadin da ta gabata.

A yayin taron addinin Kirista da aka cikin wani coci a Jihar ta Filato, Mista Young yake cewa a sanadiyar halin ko in kula gamin da rashin daukan tsauraran Matamakai daga bangaren gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya ake ci gaba da zubar da jini a kasar nan.

Mista Young ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatin Najeriya ta shimfida tsauraran matakai gami da dokoki na hukunta masu aiwatar da kashe-kashe a kasar nan.

Jakadan na kasar Amurka ya kuma nemi gwamnatin shugaba Buhari akan ta tabbatar hukumar zabe ta kasa watau INEC ta kiyaye hakikanin gaskiya gami da adalci yayin gudanar da zaben 2019.

Kazalika, jakadan na kasar Amurka ya kuma kai ziyarar ban girma gami da jinjina ga Limamin nan mai shekaru 83 a duniya, Alhaji Abubakar Abdullahi, da ya yi ceton Kiristoci 300 yayin aukuwar wani harin Makiyaya a ranar 24 ga watan Yuli cikin kauyen Nghar dake gundumar Gashish a jihar ta Filato.

Jakadan ya kuma sake jaddada sakon gaisuwa gami da jajantawa ta gwamnatin shugaban kasar Amurka, Donald Trump, dangane da aukuwar harin makiyaya cikin yankunan karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar ta Filato.
Naij.ng.


No comments:

Post a Comment