Sunday, 5 August 2018

Kasar Turkiyya ta yi wa 'yan ta'adda daurin shekaru dubu 10,557

A ranar Jumma'ar nan da ta gabata, kotu a Turkiyya ta yi wa  'yan ta'adda 36 da aka kama da laifin kai hari a tashar jiragen kasa na Ankara,babban birnin kasar,aurin rai da rai sau 101.


An cafke mutanen da ake tabbatar da cewa,suna hannu dumu-dumu a kazamin harin da ya rutsa da rayuka 100 da kuma yunkurin kashe wasu karin bayin Allah 391,wadanda a ciki har da yara kanana.

Dukannin wadanda wannan hukunci ta shafa, 'yan Haramtacciyar kungiyar ta'adda ta DAESH ne.
TRTHausa

No comments:

Post a Comment