Sunday, 19 August 2018

Kasashen duniya na ci gaba da jimamin mutuwar Kofi Annan

Kasashen duniya na cigaba da nuna alhini dangane da rasuwar tsohon babban magatakarda na MDD Kofi Annan, wanda ya rasu a yau asabar yana da shekaru 80 a duniya.


Mista Annan ya jagoranci Majalisar dinkin duniya tsakanin 1997 zuwa 2006, kuma shi ne dan asalin Afirka bakar fata na farko da ya taba rike wannan mukami a cikin wani yanayi da duniya ke fama da ringingimu iri iri.

Ana dai bayyana Mista Annan dan asalin kasar Ghana a matsayin daya daga cikin wadanda suka gudanar da jagoranci nagari a majalisar.

Gwamnatin Ghana ta sanar da ware tsawon mako daya domin zaman makoki samakon wannan rashi, yayin da kasashen duniya suka bayyana Kofi Annan a matsayin jagora abin koyi.

Shugaban Faransa Emmanual Macron ya bayyana shi da cewa mutum ne da ya yi gwagwarmaya a duk tsawon rayuwarsa, kamar dai yadda shugaban Rasha Vladimir Putin ke cewa dattijo ne kuma mai kuzari.

Jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley, ta ce har kullum duniya za ta cigaba da tuna tsohon babban magatakardar na Majalisar, yayin da Antonio Gueterres ya bayyana marigayin a matsayin da cewa mutum ne da ya yi jagoranci zuwa ga tarfaki nagari.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment