Sunday, 19 August 2018

Ko Kunsan Falalar Dake Cikin Ranar Arfa?

Kamar yadda muka sani, gobe ne Insha Allahu yinin ranar ARFA, yini mai falalar gaske, yini da dubun dubatan Al’umman musulmai da suke aikin Hajji suke haduwa a waje daya, yayinda mazauna gidajensu suke kame bakunansu da azumi.


Ranar ARFA dayane daga cikin lokuta masu tsada ga mu’umini, ma’ana dayane daga cikin lokuta masu muhimmanci da Dan Adam baida yakinin cewa zai sake riskan wannan lokaci saboda shekara guda ne. Saboda haka ne ma yasa muke kira da kada mutum yayi wasa da wannan yini mai matukar Muhimmanci saboda ba dole bane in ranan ya kewayo mutum ya kasace yana da rai kuma yana da lafiya.

Hadisi ya tabbata cikin Sahihu Muslim daga Abu Qatada Al-ansari Allah ya kara masa yadda yace Manzon Allah SAW yana cewa  “Azumtan wuni na ARFA ga wadanda ba su je aikin Hajji ba Allah zai kankare Zunubin wanda yayi wannan azumi na shekarar da ta gabata da kuma shekarar da zata zo”.  Idan ance Zunubai anan, ana nufin kananan Zunubbai. #Muslim 

Har ila yau, Hadisi ya tabbata a cikin Sahihu Muslim, Manzon Allah SAW yana cewa ‘Babu wuni da Allah yafi ‘yanta bayinsa daga wuta zuwa aljanna kamar ranar ARFA.’ #Muslim 

Addu’a  a ranar ARFA abun karbane sosai matukar mutum ya cika sharuddan Addu’a.  Allah SWT yana gaggawan karban Addu’an bawa a ranan ARFA muddin mutum ya cika sharuddan addu’a. menene Sharuddan Addu’a anan? An karbo hadisi daga abu Huraira Allah ya kara masa yarda yace: Manzon Allah SAW ya ambaci wani mutum da yake kan hanya (yana cikin tafiya) Mafirgicin kama mai kura-kura yana daga hannayan sa sama yana cewa; Ya Ubangiji na! Ya Ubangiji na! amma abincinsa Haram ne, Abun shansa haram ne, suturarsa haram ne, sannan yayi guzuri da haram. Shin tayaya za’a Amsa masa addu’arasa?” #Muslim. 

Lura da wannan Hadisi ya ‘yan Uwa yana nuna mana cewa Shiga cikin haram na daya daga cikin abubuwa ko kuma muce Ummul aba’is na kin karban Addu’a. dolene mu nisanci abubnda Allah ya haramta kamar yanda yazo a cikin hadisi  Haram a bayyane yake haka kuma halal a bayyane yake, a cikin wannan Hadisi Manzon Allah SAW yana cewa ‘ ku saurarara! Kowani sarki yana da iyaka, sai dai Allah iyakarsa itace abunda ya Haramta’ #Bukhari. 

Manzon Allah (SAW) Yace “Mafi Alkhairin addu’a itace addu’ar Arafa, kuma mafi falalan Abinda na fada ni da Annabawan da sukazo kafin ni shine “LA’ILAHA ILALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WAHUWA ALA KULLI SHAI’IN QADEER”.

Saboda haka ‘Yan Uwa muyi
kokari mu dage da fadar
wannan Azkhar A wannan rana
ta Arfat domin neman Babban
Rabo daga Allahu (S.W.T)

Ranar ARFA na daga cikin Kwanaki sanannu na watan Zulhijja da Allah ya ambace su a cikin Al-Qur’ani. #Hajji-28

Ranar ARFA itace mafi girma cikin kwanaki da Allah yafison aiyukan alkhairi a cikinsu. #Albani-irwa’I’ll ghalil.

Lura da wadannan falaloli da wannan rana mai daraja yake dauke da su,  ya kamata al’umman musulmai su dage da neman falalar Allah musamman a wannan rana, musulmi ya dukafa da yin addu’a da kuma yin ibada, musulmi ya kiyayi aikata duk wani aiki na sabon Allah komin kankantanshi, musulmi ya kasance mai Azumi a wannan rana muddin Allah Madaukakin sarki ya bashi iko.

Haka kuma kada mu manta da Kabbarori wanda tun farkon kwanaki goman nan ana bukatan muna yin su. 

Ya Allah ka nuna mana ranar ARFA muna masu koshin lafiya da aminci, Allah Ka amsa mana Addu’o’inmu, Ya Allah Ka azurtamu da gafarar nan da Ka keyi wa Bayinka a wannan wuni.

Za a iya samun marubuci a: 
+2348106792663 (text)
isamahmud77@gmail.com  
Facebook: www.facebook.com/mahmud.isa.752
Ta hanyar Rariya.

No comments:

Post a Comment