Saturday, 25 August 2018

Kocin Najeriya ya fara kokarin sanya Moses ya janye ritayarsa

Rahotanni daga Najeriya sun ce mai horar da kwallon kafa na kasar Gernot Rohr da kuma hukumar kwallon kafa ta kasar NFF sun fara tuntubar matashin dan wasan Super Eagles mai da ke kungiyar Chelsea Victor Moses, da ya janye ritayar da ya yi daga bugawa Najeriya wasa.


A kwanakin da suka gabata ne Moses’ ya bayyana matakin yin ritaya daga bugawa Najeriya wasa, lamarin da yazo wa mai horar da Super Eagles Gernot Rohr, hukumar NFF dama magoya bayan dan wasan a bazata.

Moses mai shekaru 27, ya ce ya yanke shawarar ritaya daga buga wasa a matakin kasa da kasa ne, domin mayar da hankali, wajen samun nasarori a wasannin da yake bugawa kungiyarsa ta Chelsea, sai kuma mayarda hankali wajen kula da iyalansa.

A jiya Alhamis ne Gernot Rohr ya ce zai ci gaba da tuntubar Victor Moses, domin cimma nasarar sauya shawarar dan wasan wajen yiwa tawagar Super Eagles kome.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment