Sunday, 5 August 2018

Korea ta Arewa ba ta daina kera muggan makamai ba>>MDD

Wani rahoton majalisar dinkin duniya, MDD da ya bayyana ga maneman labarai, ya ce Korea ta Arewa bata dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya da manyan makamai masu linzami ba.


Rahoton wanda wata tawagar kwararru ta majalisar dinkin duniyar ta shafe watanni 6 tana tattarawa, ya kara da cewa, Korea ta Arewan ta na ci gaba da karya takunkuman da kwamitin tsaro na Majalisar ya kakaba mata musamman ta fannin cinikin makamai da man fetur.

A cewar rahoton Korea ta Arewa tana aiki da gwamnatin Syria, domin taimaka mata ta fuskar soji, zalika tana kuma saida makamai ga mayakan ‘yan tawayen Houthi da ke kasar Yemen.

A gefe guda, rahoton ya kuma bankado cewa a tsakanin watan Oktoba na 2017 zuwa Maris na 2018 da muke ciki, Korea ta Arewa ta yi fasa kaurin saida kayayyakin da suka shafi na sawa da darajarsu ta haura dala miliyan 100 a kasashen, China, Ghana, India, Mexico, Sri Lanka, Thailand, Turkiya da kuma Uruguay.

Rahoton ya zo ne a dai dai lokacin da kasashen Rasha da China ke fafutukar ganin, kwamitin sulhu ko na tsaron majalisar dinkin duniya, ya tattauna kan batun sassauta takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta jagoranci kakabawa Korea ta Arewa, a dalilin shirinta na kera makaman nukiliya da kuma manyan makamai masu linzami.
RFIhausa

No comments:

Post a Comment