Thursday, 16 August 2018

Kotu Ta Nemi A Biya Diyya Ga Wata Musulma Bisa Kin Yin Masabaha Da Namiji

Wata Musulma ‘yar kasar Sweden ta samu nasara a kotu kan tuhumarta da kin mika hannu ta gaisa da wani namiji lokacin da aka yi mata jarabawar daukar aiki. 


Farah Alhajeh, mai shekara 24, tana neman aikin fassara ne a wani kamfani,lokacin da ta ki amincewa ta gaisa da mutumin da ke jagorantar jarabawar daukar aiki saboda tsoron kada ta saba wa addininta.

A ranar Alhamis ne wata kotun ma’aikata ta kasar ta yanke hukuncin cewa an nuna wa Farah bambanci kuma ta umarci kamfanin da ya biyata diyyar dala 4,350 (kimanin naira miliyan daya da rabi).
BBChausa.

No comments:

Post a Comment