Saturday, 4 August 2018

Kotun kasa-da-kasa ta kunyata fadar shugaba Muhammadu Buhari

Kotun kasa-da-kasa ta International Criminal Court (ICC) a takaice ta fito ta karyata batun da fadar shugaban kasar Najeriya tayi na cewa ta gayyace shugaban kasar ne ya gabatar da makalar sa a kotun saboda tsabar gaskiyar sa.


A baya dai in mai karatu zai iya tunawa, dan majalisar wakilan nan kuma na hannun damar shugaban kasa, Abdulmumini Jibrin da kuma hadiman shugaban kasar suka bayyana a wacan lokacin cewa wai tsabar gaskiyar shugaban kasar ne ta sa kotun ta gayyace shi.

sai dai kotun ta ce ba haka bane kuma daman can tana gayyatar shugabannin kasashe akai-akai.

No comments:

Post a Comment