Saturday, 25 August 2018

Kujerar da shugaba Buhari ke kai ta jawo cece-kuce

A jiyane wannan hoton na shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karade shafukan sada zumunta da muhawa inda aka nuna shugaban a hoton zaune kan wata tsohuwar kujera data fara kodewa, wannan lamari ya dauki hankulan mutane inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.Wasu daga cikin masoya shugaban kasar sun bayyana wannan abu da cewa saukin kaine da kuma alamar cewa shi ba barawon dukiyar kasa bane ko kuma babu burin tara abin Duniya a gabanshi.

Wasu kuwa, musamman 'yan adawa, sun bayyana hakan da cewa zabene ya kusanto shiyasa shugaban yake neman hanyar kasara samun amincewar mutane su sake zabenshi.

Ko da a ranar Babbar Sallah data gabata saida aka samu makamancin wannan lamari inda bayan kammala sallar idi shugaban yayi tattaki a kafa wanda masu magana da yawunshi suka bayyana hakan a matsayin bajinta.

'Yan adawa kuwa sun fito suka soki wannan lamari. Daga baya dai shugaban ya fito yace beyi wannan tattaki dan ya birge kowa ba.

No comments:

Post a Comment