Wednesday, 29 August 2018

Kwallon da Ronaldo yaci da watsiya tazo ta daya

Kwallon Cristiano Ronaldo da ya ci Juventus da watsiya lokacin yana Real Madrid a wasan kusa dana kusa dana karshe ce tazo ta daya a kwallaye mafi kyawu da akaci a gasar cin kofin zakarun turai da aka kammala.


Bayan sanar da cewa kwallon tashi ce tazo ta daya, Ronaldo ya fito ta dandalinshi na sada zumunta ya godewa masoyanshi da suka zabi kwallon a matsayin ta daya, ya kuma ce bazai taba mantawa da wannan lokaci ba, musamman abinda masoya kwallon sukayi a lokacin.

Bayan cin wannan kwallo dai masoyan kungiyar ta Juventus sun tashi tsaye sannan suka tafawa Ronaldo akan wannan kwallon duk da cewa su akaci.

No comments:

Post a Comment