Tuesday, 28 August 2018

Kwankwaso tamkar ciwon kasane a gareni>>Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kwatanta tsohon gwamnan jihar kuma Sanata a majalisar dattijan Najeriya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso da matsayin ciwon daji watau kansa.


Haka zalika gwamnan jihar ya bayyana cewa ranar da tsohon uban gidan nasa ya bar jam'iyyar APC ya koma PDP bai yi bacci ba saboda murna don kuwa daman ya zamar masa kadangaren bakin tulu ne.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu jiga-jigan tafiyar sa a gidan gwamnati jihar lokacin da suka kai masa ziyarar ban girma da kuma barka da Sallah.

Gwamnan ya kara da cewa shi Kwankwaso ya cika son kan sa don haka ne kuma ya yanke shawarar datse duk wata hulda dake a tsakanin su.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment