Friday, 17 August 2018

Kwankwaso ya hadu da matukin jirgin sama daya dauki nauyin karatunshi

Masu iya magana sukace, Alheri dankone, baya faduwa kasa banza, irin abinda ya faru da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kenan a yau, lokacin da yake kan hanyarshi ta zuwa Abuja ya hadu da daya daga cikin wadanda ya dauki nauyin karatunsu suka zama matukan jirgun sama lokacin yana gwamnan Kano.Da yake bayyana farin cikinshi da wannan lamari, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa, yana jinjinawa kamfanin Azman daya dauki daya daga cikin matasan da shi Kwankwason ya dauki nauyin karatunsu aiki, me suna Muhammad Aminu.

Yayi kira ga sauran kamfanonin jirgin sama da su baiwa irin wadannan mata sa irin wannan dama.

No comments:

Post a Comment