Thursday, 23 August 2018

Kwankwaso ya maida martani game da kalaman Ganduje na shigar sa Kano

Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata a halin yanzu dake wakiltar jihar a majalisar dattijai, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ya bayyana kalaman Gwamna Ganduje na cewar ba zai iya shiga Kano ba a matsayin abun dariya.


Sanata Kwankwaso ya yace gwamna Ganduje yaron dan siyasa ne da ba zai iya fitowa yayi siyasa da kafafun sa ba sai ya labe bayan Shugaba Buhari domin yasan bai da magoya baya.

Sanatan yayi wadannan kalaman ne a ta bakin mai magana da yawun sa Kwamared Abdulsalam inda ya kuma ce Gandujen yanzu haka a firgice yake saboda batun shigar ta Kwankwanso a garin na Kano.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment