Friday, 3 August 2018

Leicester ta cika min burina na rayuwa, zan kuma ci gaba da kallo da goyon bayansu>>Ahmed Musa

A yau, Juma'ane labarin komawar tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa kungiyar kwallon Alnassr ta kasar Saudiyya da buga wasa daga Leicester ta kasar Ingila ya bayyana, A sakon bankwana daya yiwa tsohuwar kungiyar tashi, Ahmed Musa yace zai ci gaba da kallonsu da kuma goyon bayansu.Ahmed Musa yace yana godewa duk wadanda ke kungiyar Leicester da suka sanya yaji dadin zama a Ingila. Duk da cewa ban dade ba amma na samu ilimi wanda zanci gaba da amfana dashi har abada. Yace babban abinda yake yabawa wanan kungiya ta Leicester dashi wanda har abada bazai mantaba shine bashi famar da sukayi na cikar burinshi na buga wasa a gasar Firimiya ta kasar Ingila. Ina muku fatan samun nasara zan kuma ci gaba da kallo da kuma goyon batanku.

No comments:

Post a Comment