Thursday, 30 August 2018

Luka Modric ya lashe gwarzon UEFA 2017/18: 'Ba'ayi adalci ba Ronaldo ne ya kamata ya lashe wannan kyautar'

Bayan lashe kwallon zinare saboda kyakkyawar rawar da ya taka a gasar cin kofin Duniya ta 2018 da aka kammala, dan wasan Real Madrid, Luka Modric ya kuma lashe kyautar gwarzon UEFA 2017/18, ajin maza inda ya doke Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah.


Yawancin wanda suka lashe kyautukan na UEFA 2017/18 duk daga kungiyar Real Madrid suka fito, Madrid dai ta lashe kofin sau uku a jere.

Haka kuma Modric ne ya lashe tauraron dan wasan tsakiya na UEFA.

Sai kuma Sergio Ramos da ya lashe kyautar gwardon dan wasan baya na UEFA.

Golan Madrid din, Keylor Navas ne ya lashe kyautar gwarzon Gola na UEFA.

Sai kuma tsohon dan wasan Madrid din, Cristiano Ronaldo wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gaba na UEFA.

Sai kuma kyautar shugaban UEFA da aka baiwa tsohon dan kwallon Madrid din, David Beckham.

Saidai daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankula a gurin bayar da wadannan kyautuka sune rashin zuwan Ronaldo gurin wanda wasu ke ganin cewa wai shine yasa ba'a bashi kyautar gwarzon UEfA ba.

Saidai manajan Juventus, Bappe Moratta ya shaidawa Sky Sport Italia cewa gaskiya ba'ayi adalci a wannan bayar da kyautaba, domin kuwa Ronaldo ne ya kamata ya samu kyautar gwarzon UEFA ba Modric ba saboda gudummuwar kwallaye 15 da ya ci a gasar.

Ya kara da cewa kuma Ronaldo ne yayi abubuwan da suka fi daukar hankalin 'yan kallo a gasar ta UEFA 2017/18 gaba daya, saboda haka rashin zuwanshi gurin bayar da gasar be kamata yasa a hanashi kyautar ta gwarzon shekarar UEFA ba.

Moratta yace a yaune Ronaldo ya bayyana musu cewa bazai samu zuwa gurin bayar da gasar ba kuma ya kamata a mutunta rashin zuwan nashi amma shi tabbas Ronaldonne ya kamata ya lashe gwarzon UEFA a gurinshi.

No comments:

Post a Comment