Saturday, 18 August 2018

Madrid zata kawo Neymar

Sabbin rahotanni na cewa, kungiyar Real Madrid na shirye-shiryen sayen Neymar akan kudi Yuro miliyan 270, an ruwaito cewa tun bayan rashin nasarar da sukayi a hannun Atletico Madrid suka fara tunanin kawo Neymar din.


Tun bayan tafiyar Cristiano Ronaldo ne ake rade-radin zuwan Neymar Madrid din amma da alama yanzu maganar ta fi yin karfi.

Sky Sport ta ruwaito cewa, Madrid zata yi duk me yiyuwa dan kawo dan wasan.

No comments:

Post a Comment