Friday, 24 August 2018

Maganganun 'yan Adawa ba zasu kawar da hankalina kan ci gaba da ayyukan Alheri ba>>Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar wa jam'iyyar PDP martani, inda ya ce gwamnatinsa na bakin kokarinta wajen magance manyan kalubalen kasar.


Ya ce maganganun da jam'iyyar take yi game da gwamnatinsa ba za su "kawar da hankalin gwamnatinsa daga ci gaba da ayyukan alherin da take yi ba."

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin wata liyafa da wandansu gwamnonin jam'iyyar APC da kuma wadansu 'yan majalisa a gidansa da ke Daura ranar Alhamis.
A watan jiya ne Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da wadansu gwamnoni da kuma 'yan majalisa suka sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Kuma a kwanakin baya ne tsohon Mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar, wanda ya koma PDP daga APC, ya soki wadansu manufofin gwamnatin Buharin.

Har ila yau Shugaba Buhari ya kara jaddada cewa jam'iyyar APC ta fahimci kalubalen da kasar take fuskanta, inda ya bukaci goyon bayan al'ummar kasar wajen magance su.

"Muna farin ciki idan muka fahimci cewa jama'a na jin dadin ayyukan da muke yi. Kuma muna sane da alkawurran da muka yi lokacin zaben 2015. Ba mu kawar da hankalinmu daga kansu ba," in ji shi.

Daga nan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai kan tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

"Ko 'yan adawa ba za su dora mana laifi ba game da kokarinmu wajen gyara wadannan matsalolin."

"Za mu ci gaba da yin bakin kokarinmu a wannnan shugabancin da Allah Ya ba mu kuma muna godiya kan goyon bayan da jama'a suke ba mu," in ji shugaban.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment