Friday, 10 August 2018

Majalisa zasu dawo aiki sati mai zuwa

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Yussuf Lasun, ya sanar da cewar majalisar ta gimtse hutun da ta tafi tare da bayyana cewar zasu dawo bakin aiki ranar Talata ta sati mai kamawa.


Mista Lasun ya sanar da hakan ne ga manema labarai yau, Alhamis, a Abuja.

Kwanaki biyu da suka wuce ne wata kungiyar ‘yan majalisar wakilai (PDG) ta bayyana cewar ba zasu janye hutun da suka tafi ba matukar ana bukatar su dawo ne don a canja shugabancin majalisun tarayya ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Abuja ta hannun kakakinta, Honarabul Timothy Golu, ta bayyana cewar duk da shugabannin majalisar sun hadu domin tattauna yiwuwar dawowarsu bayan fadar shugaban kasa ta roke su, ‘yan majalisar sun bayyana cewar sai an yi masu alkawarin cewar ba za a taso da maganar canja shugabancin majalisun ba idan suka dawo.

Ana saka ran majalisar zata tattuna tare da amincewa da sabon kasafin da shugaba Buhari ke bukatar su zartar.

Daga cikin karin kasafin da shugaba Buhari ke bukatar majalisun kasa su duba cikin gaggawa akwai batun amincewa da bawa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kudin da zata gudanar da zabukan shekarar 2019 da su.
Naija.ng

No comments:

Post a Comment